Mutane kusan miliyan 2 sigari ke kashewa duk shekara

Guntun karar taba sigari
Guntun karar taba sigari AFP

Mutane miliyan 1 da dubu dari 9 ne ke mutuwa duk shekara a sakamakon ciwon zuciya da ke da nasaba da shan taba sigari, a cewar wani rahoton Hukumar Lafiya ta Duniya tare da hadin gwiwar asusun World Heart Foundation da jami’ar Newcastle, gabanin ranar tunawa da masu fama da ciwon zuciya ta Duniya da ke tafe ran 29 ga wannan wata na Satumba.

Talla

Mawallafa wannan rahoton na cewa wannan adadi ya yi daidai da mutum daya cikin 5 da ke mutuwa sakamakon ciwon zuciya, suna mai kira ga masu zukar taba sigari da su su yi ban kwana da ita don kauce wa bugun zuciya.

Sun jaddada cewa masu ta’ammali da taba sigari ne suka fi fuskantar matsanancin ciwon zuciya tun suna matasa idan aka kwatanta da wadanda ba sa zukar ta.

Ko wadanda ba sa sha dayawa, ko kuma masu sha jifa jifa, ko ma wadanda ke zama kusa da masu zukar sigari suna cikin hadarin kamuwa da cutar zuciya. To sai dai idan suka bar ta, hadarin zai ragu da akalla kashi 50 a cikin shekara guda na barin ta’ammali da ita, a cewar shugaban asusun World Heart Foundation, Eduardo Bianco.

Rahoton ya kuma nuna cewa ana samun mutane akalla dubu 200 da ke mutuwa sabili da zukar taba dangin shisha a duk shekara, saboda tana haddasa hawan jini da kuma ta’azzara ciwon zuciya.

Bugu da kari, binciken da hukumar lafiya ta duniiya ta gudanar ya gano cewa kashi 97 na mutanen da cutar corona ke kashewa, na mutuwa ne sakamakon hawan jini da ciwon zuciya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.