Babu kwararrun bakake da zasu iya aiki da mu - Walls Fargo

Bankin Wells Fargo na Amurka
Bankin Wells Fargo na Amurka REUTERS/Jeenah Moon

Shugaban Wells Fargo, daya daga cikin manyan bakunan Amurka da suka shahara a duniya, Charles Scharf, ya dora alhakin gazawar bankin wajen cimma muradunsa na tabbatar da daidaito tsakanin kabilu, kan karancin kwararru bakaken fata da za su iya aiki a karkashinsa.

Talla

Tuni dai kalamin na Scharf ya janyo masa suka gami da cece-kuce kan zargin da aka dade ana yiwa bankin na nuna wariya ga wasu jinsi ko kabilu.

A baya bayan nan ne dai aka gano wata wasikar cikin gida da shugaban bankin na Wells Fargo Charles Scharf ya rubuta, wadda cikinta yake cewa, Magana ta gaskiya itace akwai karancin bakaken fata kwararru da suka cika ka’idar cancantar aiki da su, koda yake a cewarsa, wasu za su iya zaton cewa yana neman hujjar kare kansa ko bankin ne daga zarge-zargen fifita turawa fararen fata kan bakake da kuma wasu jinsin na yankin Latin ko Asiya.

Har yanzu dai manyan jami’an bankin na Wells Fargo basu ce komai ba kan kalaman da shugaban nasu Scharf ya furta kan bakar fatar a baya bayan nan, sai dai sun ce a halin yanzu babban abinda jagoran nasu yasa a gaba, shi ne cimma marudun daidaito tsakanin jinsi daban daban a wajen shugabancin bankin.

Yanzu haka gwamnatin California a Amurka inda Hedikwatar bankin na Wells Fargo take, na shirin kafa dokar tilastawa dukkanin Kamfanonin dake jihar bada akalla mukamin darakta daya ga jinsuna marasa rinjaye a hukumar gudanrwarsu nan da shekarar 2021, muradin da tuni bankin ya cimma, bayan bada mukaman daraktoci ga bakar fata da kuma wani daga yankin latin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.