Duniya-Lafiya

Coronavirus ka iya lakume rayukan mutane miliyan 2 - WHO

Babbar makabartar birnin Sao Poulo daake binne wadanda annobar coronavirus ta halaka.
Babbar makabartar birnin Sao Poulo daake binne wadanda annobar coronavirus ta halaka. REUTERS/Amanda Perobelli

Wani sabon rahoton hukumar lafiya ta duniya WHO yayi gargadin cewa annobar coronavirus ka Iya halaka mutane miliyan 2, muddin kasashe da sauran hukumomi suka gaza hada kai wajen daukar matakan dakile cutar.

Talla

Gargadin WHO na zuwa a daidai lokacin da annobar ta sake barkewa karo na 2 a wasu sassan duniya, bayan saukin da aka samu a baya.

Yanzu haka dai adadin rayukan da annobar ta coronavirus ta halaka na gaf da kaiwa miliyan 1, kusan watanni 10 bayan bullar ta daga China.

Alkaluman hukumar lafiyar ta duniya na baya bayan nan sun kuma nuna cewar akalla mutane miliyan 32 da dubu 300 suka kamu da cutar a tsakanin kasashe kusan 200, sai dai daga cikinsu akalla miliyan 24 sun warke.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.