Iran-Amurka

Amurka ta janyo mana hasarar dala biliyan 150 - Iran

Shugaban kasar Iran Hassan Rouhani.
Shugaban kasar Iran Hassan Rouhani. Iranian Presidency / AFP

Shugaban Iran Hassan Rouhani ya zargi Amurka da mugunta dalilin takunkuman karya tattalin arzikin da ta yi gaban kanta wajen sake kakaba mata a makon jiya.

Talla

Yayin jawabi cikin fushi a jiya asabar, shugaban na Iran ya bayyana takunkuman na Amurka a matsayin ta’addanci, wanda kawo yanzu ya janyo musu tafka hasarar dala biliyan 150.

A ranar Asabar 20 ga watan Satumban nan cikin yanayi na bazata Amurka ta yi gaban kanta wajen sanar da sake laftawa Iran dukkanin takunkuman karya tattalin arzikin da aka taba kakaba mata, wadanda daga bisani aka janye su, bayan cimma yarjejeniya kan shirin nukiliyarta da manyan kasashen Duniya a shekarar 2015.

Matakin Amurka ya sake dagula lamurra tsakaninta da Iran, wadda dama tuni dangantakarsu ta yi tsami, bayan da a shekarar 2018, shugaba Trump ya janye daga yarjejeniyar nukiliyarta ta 2015, tare da kakaba mata wasu takunkumai, wanda manyan kasashe Turai ciki har da Birtaniya, Jamus da Faransa suka bijirewa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.