Iran ta sake kera makami mai linzami mai cin zangon sama da kilomita 700

Wani makami mai linzami kenan da Iran ta kera
Wani makami mai linzami kenan da Iran ta kera Nazanin Tabatabaee Yazdi/TIMA via REUTERS

Rundunar Sojin Iran ta gabatar da wani sabon makami mai linzami da ta kera wanda ke iya cin zangon sama da kilomita 700.

Talla

Makamin da aka yi wa lakabi da Zolfaghar Basir, wani sabon makami ne da gudunsa ya zarta na sauran makaman da kasar ta mallaka, cikin su harda Hormuz-2 wanda ke cin zangon kilomita 300 da kasar ta gwada a watan Maris na shekarar 2017.

Kwamandan zaratan sojin kasar, Janar Hossein Salami ya bayyana gabatar da makamin a matsayin wani gargadin domin razana abokan gabar Iran.

Kawo yanzu babu ciakkken bayani kan ko hukumomin tsaron na Iran sun yi gwajin sabon makamin , amma wasu hotuna da Kamfanin Dillancin Labaran kasar Tasnim ya wallafa, sun nuna yadda aka daidaita makamin akan wata katuwar motar cilla makamai.

A shekarar 2017 da 2018, jami’an tsaron Iran sun yi amfanin da nau’in makamkin na Zolfaghar wajen kaddamar da harin ramuyar gayya kan mayakan ISIS na Syria.

Kazalika Iran din ta sake yin amfani da makamakin a cikin watan Janairu wajen kai hari kan sansanonin da ke dauke da sojojin Amurka a Iraqi da zummar daukar fansar kisan da Amurka ta yi wa kwamandan sojinta, Qasem Soleimani a Baghdad.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.