Trump ya kauce biyan wasu haraji kafin zabensa

Shugaban Amurka Donald Trump.
Shugaban Amurka Donald Trump. AP/Evan Vucci

Rahotanni daga Amurka sun ce shugaba Donald Trump ya kwashe dogon lokaci yana kaucewa biyan haraji ko kuma biyan wasu yan kudade kadan sabanin abinda dokar kasa ta tanada, har zuwa lokacin da ya zama shugaban kasa.

Talla

Jaridar New York Times ta ruwaito cewar attajirin shugaban ya biya Dala miliyan 750 kawai harajin tarayya a shekarar 2016, lokacin da ya lashe zaben shugaba kasa, sai kuma shekarar 2017, amma babu shaidar biyan haraji na shekaru tsakanin 10 zuwa 15, saboda abinda ya kira asarar kudaden da yake samu.

Shugaban ya musanta zargin, yayin da shugabar Majalisar wakilai Nancy Pelosi ta zarge shi da rashin mutunta dokar kasa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.