Amurka

Trump da Biden na shirin tafka muhawara zagayen farko gabanin zabe

Ana tsammanin Trump ya yi amfani da gogewarsa a fannin caccaka wajen caccakar Joe Biden a muhawarar ta yau.
Ana tsammanin Trump ya yi amfani da gogewarsa a fannin caccaka wajen caccakar Joe Biden a muhawarar ta yau. REUTERS/Brian Snyder

‘Yan takarar shugabancin Amurka za su fara tafka muhawara yau Talata a zagayen farko na jerin muhawara 3 da za su yi gabanin zaben kasar na watan Nuwamba mai zuwa, inda za a kara tsakanin shugaba mai ci Donald Trump da tsohon shugaban kasar Joe Biden na jam’iyyar demokrat.

Talla

Muhawarar wadda za ta gudana ta kai tsaye a gidajen talabijin na kasar, a wannan karon za a takaita yawan mutanen da za su halarci zauren mahawarar haka, zalika ba a sahalewa ‘yan takarar biyu musabaha gabanin hawa dandalin ba, sabanin yadda aka saba.

Mahwarar bisa jagorancin Chris Wallace na gidan talabijin din Fox, da za ta dauki tsawon mintuna 90 manufarta shi ne bude hanya ga Amurkawa don gane wanda ya cancanci jagorantar kasar tsakanin shugaba mai ci Donald Trump na jam’iyyar Republican mai shekaru 74 da kuma Joe Biden na jam’iyyar Demokrat mai shekaru 77.

Ana dai ganin yayin muhawarar Trump wanda ke da cikakkiyar gogewa ta sukar abokin hamayya, zai yi amfani da ikirarinsa na baya-bayan nan da ke cewa kwakwalwar Joe Biden ba ta aiki yadda ya kamata, tare da neman ayi masa gwaji don tabbatar da kwakwalwar ba ta mutu ba baya ga zarginsa da tu’ammali da miyagun kwayoyi.

A bangare guda shima Biden wadda kuri’ar jin ra’ayin jama’a ta nuna shi ne tauraron Amurkawa a yanzu zai soki Trump dinne ta hanyar kafa hujja da rahoton baya-bayan da jaridar New York Times ta wallafa da ke nuna yadda shugaban mai ci ya share tsawon lokaci ba tare da biyan haraji ba, batun da ke matsayin babban laifi ga dokokin kasar.

Haka zalika, tun bayan da muhawarar ta karato Biden ya matsa lamba kan yadda Trump ya yi sakacin salwantar rayukan Amurka saboda rashin daukar matakan da suka kamata yayin bullar annobar Covid-19.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.