An nada Sheikh Al-Sabah a matsayin sabon sarkin Kuwait

Sarkin Kuwait Sabah al-Ahmad al-Sabah
Sarkin Kuwait Sabah al-Ahmad al-Sabah REUTERS/Kevin Lamarque

An nada Sheikh Nawaf al-Ahmad Al-Sabah a matsayin sabon sarkin Kuwait, wanda ya maye gurbin dan uwansa sarki Sheik Sabah al-Ahmad Al-Sabah da Allah yayi rasuwa yana mai shekaru 91 a duniya.  

Talla

Shugabannin Kasashen duniya na cigaba da aikewa da sakon ta’aziyar rasuwar Sarki Sabah al-Ahmad Al-Sabah na Kuwait wanda ya rasu jiya yana da shekaru 91 a duniya, yayin da ake saran rantsar da dan uwan sa mai shekaru 83 Yarima Sheikh Nawaf al-Ahmad Al-Sabah a matsayin wanda zai maye gurbin sa.Tuni Gwamnati ta bayyana zaman makoki na kwanaki 40.

Marigayi sarki Cheik Sabah al-Ahmad al-Sabah ya samu yabo matuka saboda salon iya mulki da tattalin zaman lafiya a kasashen labarawa.

Gwamnatin kasar ta ware kwanakin 40 na zaman makoki saboda wannan rashi da aka samu.

Tuni kasashen duniya da kungiyoyi suka fara aike da sakon ta’aziyyarsu, Majalisar Dinkin Duniya cikin sakon ta’aziyarta ta bayyana marigayi sarki amatsayin mai son hadin kan al’umma da zaman lafiya.

Babban magatakardar Majalisar Dinkin Duniya da ya sa hannun kan sakon ta’aziyar yace, duniya bazata taba mantawa da sarki ba a kokarin da yakeyi kulla yaumin domin hada kan larabawa.

Shima Franministan Burtaniya Boris Johnson a sakon ta’aziyarsa yace duniya zata ci gabata tuna marigayi Cheik Sabah al- Ahmad al-Sabah saboda irin gudunmuwarsa a fannoni da dama.

Mariyagayin wanda ya mulki Kuwait tun a shekarar 2006, ya rasune a wani asibi dake kasar Amurka inda yayi fama da jinya.

Marigayi Cheik Sabah al- Ahmad al-Sabah shine sarki na 15 a gidan sarautar Kuwait, da suke rike da mulkin kasar shekaru kusan 250 da suka gabata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.