Faransa-Armenia

Macron ya caccaki Turkiya saboda Azerbaijan

Shugaban Faransa Emmanuel Macron
Shugaban Faransa Emmanuel Macron Ludovic MARIN / AFP

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya caccaki Turkiyya a game da abin da ya kira rashin dattaku a kalaman da ta yi na nuna goyon baya ga yunkurin Azerbaijan na kwace yankin Karabakh da ya balle daga cikinta.

Talla

Macron ya yi wannan caccakar ce a birnin Riga ta kasar Latvia yayin ganawa da manema labarai, inda ya ce kalaman na Turkiyya na da matukar hatsari.

Turkiya ta mayar da martani, inda ta zargi Macron da goyon bayan mamayar da Armenia ta yi wa yankin da ake gwabza fada a kai tun daga ranar Lahadin da ta gabata.

Faransa da Turkiyya dai na da jikakka a game yankin gabashin Mediterranean mai arzikin makamashi, da kuma Libya har da wasu sassa na Gabas ta Tsakiya.

Ministan Harkokin Wajen Turkiya, Mevlut Cavusoglu ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labaran kasar cewa Turkiya ba ta gaba da Faransa, amma kuma goyon bayan da shugaba ke bai wa Armenia na nuni da cewa ya goyi bayan mamayar da ta yi.

Macron dai ya ce zai yi wa shugaba Vladimir Putin na Rasha bayanin halin da ake ciki a Karabakh a Laraban nan, sannan a ranar Alhamis ya gana da Donald Trump na Amurka duk a kan batun.

Armenia da Azerbaijan sun shafe gwamman shekaru suna baiwa hammata iska a kan yankin Karabakh.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.