MDD

MDD na neman Dala biliyan 15 na yaki da corona

Antonio Guterres, Sakataren Majalisar Dinkin Duniya.
Antonio Guterres, Sakataren Majalisar Dinkin Duniya. REUTERS/Lisi Niesner

Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci gaggauta zuba Dala biliyan 15 a wani asusun kasashen duniya domin samar da kuma rarraba riga-kafin cutar coronavirus a sassan duniya.

Talla

Hadakar Kasashen Duniya mai yaki da cutar Covid-19 karkashin jagorancin Hukumar Lafiya ta Duniya, ta samu kimanin Dala biliyan 3 daga cikin Dala biliyan 38 da ake bukata domin cimma bukatar duniya ta samarwa da kuma rarraba riga-kafin coronavirus har guda biliyan 2 nan da shekarar badi.

Kazalika wannan hada na fatar yi wa mutane miliyan 245 magani da kuma gudanar da gwaje-gwaje har guda miliyan 500 na da shekarar 2021.

Daga cikin manyan alkawuran da aka yi na cika wannan asusun na duniya, har da karin tallafin Euro miliyan 100 da shugabar Gwamnatin Jamus Angela Merkel ta ce za ta bayar duk da cewa a can baya kasarta ta sanar da aniyar bada tallafin Euro miliyan 675.

Ministan Harkokin Wajen Birtaniya, Dominic Raab ya ce, kasarsa wadda tuni ta yi alkwarin Pam miliyan 250, za ta kashe karin Pam miliyan 250.

Firaministan Sweden Stefan Lofven ya yi alkawarin bada Dala miliyan 10, yayin da takwaransa na Canada, Justin Trudeau ya ce, za su bada Dala miliyan 440.

Shugaban Bankin Duniya, David Malpass ya yi tayin bada kimanin Dala biliyan 12 ga kasashen duniya domin samarwa da kuma rarraba riga-kafin Covid-19.

Sakatere Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres ya bayyana cewa, ana bukatar wadannan kudade domin gaggauta samar da riga-kafin cutar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.