Armenia-Azerbaijan

Shugabannin duniya sun tsoma baki a rikicin Karabakh

An tabbatar da mutuwar mutane akalla 130 kawo yanzu a rikicin Armenia da Azerbaijan
An tabbatar da mutuwar mutane akalla 130 kawo yanzu a rikicin Armenia da Azerbaijan Handout / Armenian Defence Ministry / AFP

Shugabannin kasashen Rasha da Amurka da Faransa sun bukaci tsagaita musayar wuta a yankin Nagorny Karabakh, suna masu kira ga Armenia da Azerbaijan da su shiga tattaunawar sulhu ba tare da jinkiri ba ko kuma kindaya ka’idoji.

Talla

A cikin wata sanarwa da suka fitar a wannan Alhamis, shugaban Faransa Emmanuel Macron da takwarorinsa na Rasha da Amurka, wato Vladimir Putin da Donald Trump sun bukaci gaggauta kawo karshen tsamin dangantaka tsakanin sojojin da ke gwabza yaki a yankin Nagorny Karabakh.

Shugabannin kasashen uku wadanda ke jagorancin Kungiyar OSCE Minsk da ta taka rawa wajen kawo karshen rikicin Armenia da Azerbaijan a tsakankanin shekarun 1990, a wannan karo sun bukaci bangarorin biyu da su koma teburin sulhu domin cimma matsaya mai dorewa.

Sanarwar dai ta ce, dole ne a gudanar da wannan tattaunawar sulhun cikin kyakkyawan kudiri ba tare da zayyana wasu sharudda ba, sannan kuma a gudanar da ita karkashin jagorancin Kungiyar OSCE Minsk.

Kungiyar ta Minsk wadda aka kafa ta a shekarar 1992, ta sha sanya ido kan tarukan da suka gudana tsakanin shugabannin Armenia da Azerbaijan, amma dai ta gaza wajen samar da zaman lafiya mai dorewa tsakanin kasashen biyu.

A karshen makon da ya gabata ne, dauki-ba-dadi mai tsanani ya sake barkewa tsakanin kasashen biyu, inda kawo yanzu aka tabbatar da mutuwar mutane akalla 130 a daidai lokacin da rikicin ya shiga kwana na biyar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.