Amurka ta rage yawan bakin da za ta rika karba duk shekara zuwa dubu 15

Wasu 'yancirani da ke kokarin shiga Amurka daga Guatemala.
Wasu 'yancirani da ke kokarin shiga Amurka daga Guatemala. Johan ORDONEZ / AFP

Shugaba Donald Trump ya zabtare adadin ‘yan gudun hijirar da Amurka ke karba zuwa kimanin dubu 15, yayin da ya yi kakkausar suka ga ‘yan gudun hijirar da suka fito daga Somalia da sauran kasashen da rikici ya daidaita.

Talla

Duk da yadda Duniya ke fuskantar yawaitar mutanen da rikici ke rabawa da muhallansu saboda tashe-tashen hankulan da kasashe ciki, gwamnatin ta Trump ta tsaya kai da fata cewa 'yan gudun hijira dubu 15 kadai za ta bai wa damar kwarara cikin kasar a kowace shekara.

Matakin gwamnatin na Trump da ma’aikatar harkokin wajen Amurka ke sanarwa a jiya Alhamis na zuwa ne dai dai lokacin da ya rage sa’o’i kalilan kasar ta fara amfani da sabuwar kalandar kasafin kudi.

Trump wanda ya gina gangamin yakin neman zabensa kan sukar hukumar shige da ficen kasar tun farkon shekarar nan ya dakatar da karbar baki inda ya fake da annobar Coronavirus.

Gabanin rage yawan 'yan gudun hijirar a bana zuwa dubu 15 a shekarar da ta gabata ne Donald Trump ya fara rage yawan bakin da kasar za ta rika karba duk shekara zuwa dubu 18 sabanin dubu 100 da ta ke karba a baya lokacin mulkin tsohon shugaban kasar Barrack Obama.

Sanarwa da fadar White House ta fitar dangane da matakin ta ce Amurka a shirye ta ke ta tallafawa mutanen da ke bukatar agaji a kasashensu bai sai sun kai ga shigo mata ba, ta hanyar magance musu rikice-rikicen da suke fama da su.

Tuni dai shugaban hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Amurkan Eric Schwartz ya yi tir da matakin na Trump yana mai bayyana matakin da batu mai matukar sosa zuciya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.