Amurka

Trump ya kamu da cutar coronavirus

Shugaban Amurka Donald Trump da matarsa sun kamu da cutar coronavirus kamar yadda ya sanar a shafinsa na Twitter.

Shugaban Amurka Donald Trump.
Shugaban Amurka Donald Trump. REUTERS/Tasos Katopodis
Talla

Shugaba Donald ya kamu da cutar coronavirus ne bayan daya daga cikin mashawartansa na kusa wato Hope Hicks ta fara harbuwa da cutar.

Hicks mai shekaru 31, ta yi balaguro tare da shugaba Trump a jirgin Air force One zuwa jihar Ohio a farkon wannan makon, inda suka halarci muhawarar da aka tafka tsakanin Trump da abokin takarararsa na jam’iyyar Democrat Joe Biden.

Yanzu haka fadar gwamnatin White House ta dakatar da yakin neman zaben shugaban wanda aka shirya gudanarwa a Florida a wannan Juma’ar sakamakon kamuwa da cutar.

Shugaba Trump dai zai ci gaba da killace kansa a fadar White House har zuwa lokacin da ake fatan zai warke daga cutar.

Likitocin fadar White House sun ce, Trump da matarsa na cikin yanayi mai kyau, kuma shugaban zai ci gaba da gudanar da aikinsa daga fadar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI