India

Coronavirus ta kashe mutane sama da dubu 100 a India

An yi hasashen cewa India za ta zarta Amurka wajen yawan masu dauke da coronavirus nan kusa.
An yi hasashen cewa India za ta zarta Amurka wajen yawan masu dauke da coronavirus nan kusa. Francis Mascarenhas/Reuters

Adadin mutanen da coronavirus ta hallaka a India ya zarta dubu 100 a yau Asabar kamar yadda kididdigar hukumomin kasar ta nuna, yayin da cutar ke ci gaba da barna a kasar wadda ita ce ta biyu mafi yawan al’umma a duniya.

Talla

A jumulce, mutane dubu 100 da 842 suka mutu bayan kamuwa da cutar a India , abin da ya sa kasar ta zama ta uku a jerin kasashen da annobar ta fi lakume rayuka, inda take biye da Amurka da Brazil.

Mutane miliyan 6 da dubu 470 suka harbu da kwayar cutar ta coronavirus a kasar kadai, kuma a halin yanzu ta kama hanyar zarta Amurka wajen yawan masu dauke da cutar.

Ana ganin nan da ‘yan makwanni kasar za ta zarta Amurka a yawan masu fama da cutar, yayin da wasu masana kiwon lafiya ke cewa, hukumomin kasar ba su fitar da alkaluma na hakika ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.