Faransa-Italiya

Guguwa ta yi barna a Faransa da Italiya

Guguwa mai hade da ruwan sama ta yi barna a kasashen Faransa da Italiya.
Guguwa mai hade da ruwan sama ta yi barna a kasashen Faransa da Italiya. REUTERS/Aly Song

Akalla mutane biyu sun rasa rayukansu, sannan kimanin 30 sun bace bayan ruwan sama mai tafe da guguwa ya afka wa Kudancin Faransa da kuma Arewacin Italiya a yau Asabar, yayin da hanyoyi da gadoji suka lalace, baya ga dubbai da suka rasa wutar lantarki a gidajensu.

Talla

Wani ma’aikacin agaji ya rasa ransa a Italiya, yayin da shi ma wani mutun ya mutu bayan ambaliyar ruwa ta yi awon gaba da shi a cikin motarsa.

An rawaito cewa, kimanin mutane takwas suka bace a birnin Nice na Faransa, sannan 22 suka bace a kan iyakar ruwan Italiya.

Yanzu haka jami’an agajin Italiya na ci gaba da kokarin isa wani kauye a cikin jirgin kasa domin kai wa al’ummar yankin dauki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.