Amurka

Ko wani hali Trump ke ciki a asibiti?

Shugaban Amurka Donald Trump.
Shugaban Amurka Donald Trump. MANDEL NGAN / AFP

Shugaban Amurka Donald Trump na ci gaba da samun kulawa a asibiti sakamakon kamuwa da cutar COvid-19, lamarin da ya kawo masa cikas a yakin neman zabensa a daidai lokacin da ya rage wata guda a gudanar da zaben shugaban kasa.

Talla

A wani faifen bidiyo da aka nada na tsawon minti 18, an jiyo shugaba Trump na cewa, an kwantar da shi a asibiti, amma yana samun sauki a cewarsa.

A yammacin jiya Juma’a ne aka ga shugaban na ficewa daga fadar White House sanye da kyallen rufe baki da hanci, inda wani jirgi mai saukar ungulu ya dauke shi zuwa asibitin sojoji na Walter Reed da ke wajen birnin Washington.

Shugaban China Xi Jinping na cikin na baya-bayan nan da suka yi wa Trump fatar samun sauki daga wannan cuta ta coronavirus, yayin da babban abokin hamayarsa a zaben shugaban kasa, Joe Biden ya ce, yana yi masa addu’ar murmurewa.

Biden ya shaida wa masu kada kuri’a a zaben mai tafe cewa, ya sha nanata bukatar daukar cutar coronavirus da muhimmanci, inda kawo yanzu ta kashe mutane sama da dubu 208 a Amurka kadai.

Shugaba Trump ya sha yi wa Biden shagube kan yawaita sanya kyallen rufe baki da hanci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.