Amurka

Rashin lafiyar Trump ya tsananta-Majiya

Shugaban Amurka Donald Trump.
Shugaban Amurka Donald Trump. Leah Millis/Reuters

Wata majiya ta bayyana cewa, shugaban Amurka Donald Trump da ke fama da cutar coronavirus ya shiga cikin mawuyacin hali a tsawon sa’o’i 24 kuma akwai yiwuwar rashin lafiyarsa ya tsananta nan da kwanaki biyu masu zuwa a cewar majiyar.

Talla

Kodayake Fadar Gwamnatin White House ta ce, shugaban wanda ke kwance a asibitin Walter Reed na samun sauki daga toshewar hanci da tari da kuma gajiya

Shugaban dai ya samu koma-baya a yakin neman zabensa sakamakon kamuwa da cutar a daidai lokacin da ya rage wata guda cur a gudanar da zaben shugaban kasa.

A wani faifen bidiyo da aka nada na tsawon minti 18, an jiyo shugaba Trump na cewa, an kwantar da shi a asibiti, amma yana samun sauki a cewarsa.

A yammacin jiya Juma’a ne aka ga shugaban na ficewa daga fadar White House sanye da kyallen rufe baki da hanci, inda wani jirgi mai saukar ungulu ya dauke shi zuwa asibitin sojoji na Walter Reed da ke wajen birnin Washington.

Shugaban China Xi Jinping na cikin na baya-bayan nan da suka yi wa Trump fatar samun sauki daga wannan cuta ta coronavirus, yayin da babban abokin hamayarsa a zaben shugaban kasa, Joe Biden ya ce, yana yi masa addu’ar murmurewa.

Biden ya shaida wa masu kada kuri’a a zaben mai tafe cewa, ya sha nanata bukatar daukar cutar coronavirus da muhimmanci, inda kawo yanzu ta kashe mutane sama da dubu 208 a Amurka kadai.

Shugaba Trump ya sha yi wa Biden shagube kan yawaita sanya kyallen rufe baki da hanci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.