Armenia-Azerbaijan

An sake kashe sojojin Armenia 51

Armenia da Azerbaijan na amfani da muggan makamai waje kai wa juna farmaki
Armenia da Azerbaijan na amfani da muggan makamai waje kai wa juna farmaki AFP/Azerbaijani Defence Ministry/Handout

Kasar Armenia ta ce an sake kashe mata sojoji 51 a fafatawar da ake ci gaba da yi tsakanin dakarunta da na Azerbaijan dangane da rikicin mallakar yankin Nagorny-Karabakh, yayin da yakin ya shiga rana ta 7.

Talla

Gwamnatin Armenia ta wallafa sunayen dakarun da aka kashe a shafinta na intanet sa’oi bayan shugaban ‘Yan awaren yankin, Arayik Harutyunyan ya sanar da matakin karshe na shiga yaki da Azerbaijan a fagen-dagar Karabakh.

Yunkurin Majalisar Dinkin Duniya da Kungiyar Kasashen Turai da kuma shugabannin Rasha da Amurka da Faransa na ganin an tsagaita wuta tsakanin bangarorin biyu ya ci tura, ganin yadda kasashen biyu ke ta barin wuta a tsakaninsu.

Mai magana da yawun ma’aikatar tsaron Armenia, Sushan Stepanyan ta ce bangarorin biyu na amfani da manyan makamai wajen kai wa juna farmaki.

Kasashen Azerbaijan da Armenia sun kwashe shekaru da dama suna fafatawa a tsakaninsu dangane da mallakar Nagorny-Karabakh, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar akalla mutane dubu 30 tun daga shekarar 1990.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI