Amurka

Biden ya bai wa Trump gagarumar rata gabanin zabe

Joe Biden  tare da Donald Trump za su fafata da juna a zaben ranar 3 ga watan Nuwamba mai zuwa.
Joe Biden tare da Donald Trump za su fafata da juna a zaben ranar 3 ga watan Nuwamba mai zuwa. Studio Graphique FMM

Wata sabuwar kuri’ar jin ra’ayin jama’a ta nuna cewa, dan takarar shugabancin Amurka na Jam’iyyar Democrat, Joe Biden ya sha gaban abokin fafatawarsa, Donald Trump da gagarumin rinjaye.

Talla

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin shugaba Trump ke jinya a asibiti bayan ya kamu da coronavirus, yayin da akasarin Amurkawa ke cewa, shugaban ya kamu da cutar ce saboda ya ki daukar ta da muhimmanci.

Shugaba Trump ya sha yin watsi da batun tsanantar cutar, yana mai cewa, za ta bace da kanta, yayin da yake yi wa Biden isgilanci saboda yadda yake sanya kyallen rufe baki da hanci.

A ranar 3 ga watan gobe za a gudanar da zaben shugaban kasa a Amurkar, yayin da Biden ya bai wa Trump ratar maki 10 a kuri’ar jin ra’ayin jama’a ta baya-bayan nan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI