Faransa-Caledonia

Caledonia ta zabi ci gaba da zama karkashin Faransa

Al'ummar yankin New Caledonia sun fi son Faransa ta ci gaba da zama uwar gijiyarsu.
Al'ummar yankin New Caledonia sun fi son Faransa ta ci gaba da zama uwar gijiyarsu. Theo Rouby / AFP

Al’ummar New Caledonia da ke yankin Kudancin Tekun Pacific sun zabi ci gaba da zama karkashin kasar Faransa a wata kuri’ar raba gardama da suka kada a yau Lahadi.

Talla

Kimanin kashi 53.26 na al’ummar yankin suka zabi ci gaba da zama karkashin Faransa, yayin da shugaba Emmanuel Macron ya yi lale marhabin da wannan sakamako.

A karo na biyu kenan cikin shekaru biyu da mutanen yankin ke kada irin wannan kuri’ar ta jin ra’ayin jama’a, inda a shekarar 2018, masu son ci gaba da kasancewa tare da Faransa suka samu kashi 56.7 a wancan lokaci.

Yankin na New Caledonia na tsakankanin Australia da Fiji kuma tun shekarar 1853, Faransa ta karbe yankin mai dauke da al’umma dubu 270.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.