Amurka

Ina samun sauki daga Covid-19-Trump

Shugaban Amurka Donald Trump.
Shugaban Amurka Donald Trump. REUTERS/Leah Millis

Shugaban Amurka Donald Trump ya wallafa wani sakon bidiyo daga dakin jinyarsa a asibitin Walter Reed, inda yake cewa, yana samun sauki daga cutar Covid-19 kuma nan kusa zai dawo a cewarsa.

Talla

Kodayake shugaban ya ce, kwanaki masu zuwa ne za su fayyace hakikanin gwajin da aka yi masa.

Shugaban ya bayyana fatar kammala yakin neman zabensa kamar yadda ya fara.

Sai dai ko a yammacin jiya Asabar, likitan Fadar White House ,Sean Conley ya ce, har yanzu akwai sauran-rina-a- kaba dangane da rashin lafiyar shugaban.

Tun da farko makusantan Trump da suka hada da shugaban ma’aikatan fadar White House, Mark Meadows sun ce, sun shiga dimuwa a ranar Juma’a ganin halin da Trump ya shiga.

Rhotannin baya-bayan nan cewa, watila a sallame shi daga asibiti a gobe Litinin kamar yadda tawagar likitocinsa ta fadi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI