Faransa

Macron ya yi wa addinin Islama kazafi-Jami'ar Azhar

Shugaban Faransa Emmanuel Macron
Shugaban Faransa Emmanuel Macron Francisco Seco / POOL / AFP

Shehannan malaman Jami’ar Azhar ta kasar Masar sun caccaki kalaman shugaban Faransa Emmanuel Macron da suka bayyana a matsayin nuna wariya da kiyayya ga addinin Islama.

Talla

A ranar Juma’ar da ta gabata ne, shugaba Macron ya kaddamar da shirin kare manufofin Faransa da suka yi hannun riga da addini, yana mai danganta Islama a matsayin addinin da ke cikin rikici a fadin duniya.

Wata sanarwa da ta fito daga Sashen Nazari da Bincike na Jami’ar Azhar ta ce, Macron ya yi wa addinin Islama kazafi kan abin da babu kamshin gaskiya a cikinsa.

Sanarwar ta ce, kalaman Macron za su sosa ran Musulmin duniya da yawansu ya kai biliyan 2, yayin da hakan zai toshe hanyar tattaunawar fahimtar juna.

Shugaba Macron ya kuma yi gargadi game da yunkurin kirkirar wani yankin al’umma wadda za ta samar da nata ka’idojin tsakanin Musulman Faransa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI