Amurka

Ana shakku kan hakikanin halin da Trump ke ciki

Shugaban Amurka Donald Trump a cikin motar da ya yi ran-gadi a harabar asibitin Walter Reed.
Shugaban Amurka Donald Trump a cikin motar da ya yi ran-gadi a harabar asibitin Walter Reed. ALEX EDELMAN / AFP

Shugaban Amurka Donald Trump da ke fama da cutar Covid-19 na shan caccaka daga hukumomin kiwon lafiya sakamakon wani ran-gadi da ya yi a cikin mota a harabar asibitin da ke ba shi kulawa, yayin da ake shakku game da yiwuwar sallamar shi daga asibiti a wannan Litinin.

Talla

A yammacin ranar Lahadi ne shugaban ya fito daga dakin jinyarsa domin jinjina wa magoya bayansa da suka yi dafifi a wajen asibitin Walter Reed.

Trump sanye da kyallen rufe baki da hanci, ya yi ta daga hannunsa ga magoya bayan nansa, lamarin da wasu masharhanta ke cewa, an tsara wannan ran-gadin ne domin nuna wa duniya cewa, lallai yana samun sauki daga cutar Covid-19 duk da cewa, likitocinsa sun fitar da bayanan mabanbanta game da halin da yake ciki.

Har yanzu dai ana ci gaba da diga ayar tambaya kan hakikanin halin da shugaban ke ciki.

Kwararrun a fannin kiwon lafiya sun ce, ran-gadin da Trump ya yi ya saba wa ka’idar yaki da wannan cuta wadda ta lakume rayukan Amurkawa fiye da dubu 209.

Kwararrun sun ce, yanzu haka ya zama wajibi a killace mutanen da suka zauna tare da shi a cikin wannan mota ta kasaita har tsawon makwanni biyu saboda akwai yiwuwar shugaban ya sammu su cutar kuma watakila su iya mutuwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.