Armenia-Azerbaijan

Armenia da Azerbaijan sun far wa fararen hularsu

Dakarun Armenia da Azerbaijan sun zargi juna da kai wa fararen hula hari
Dakarun Armenia da Azerbaijan sun zargi juna da kai wa fararen hula hari Azerbaijan's Defense Ministry via AP

Dakarun Armenia da Azerbaijan sun yi musayar hare-haren makaman roka da atilari a daidai lokacin da barin wuta ya tsananta a tsakaninsu kan mallakar yankinn Nagorno Karabakh, yayin da kasashen biyu suka zargi juna da karkatar da hare-harensu kan wuraren da fararen hula ke rayuwa.

Talla

Gwamnatin Armenia ta ce sojin Azerbaijan sun sake yin luguden wuta kan gari mafi girma a birnin na Nagorno Karabakh wato Stepanakert a ranar lahadin, wanda tun ranar Juama’a ke shan barin wutar babu kakkautawa.

Ita kuwa ma’aikatar tsaron Azerbaijan cewa ta yi birnin Ganja mai yawan mutane akalla dubu 330 da ke yammacinta ne, dakarun Armenia suka afkawa a ranar Lahadi, inda dakarun abokan gabar suka yi ikirarin lalata fiin jiragen yakin kasar.

Dukkanin kasashen biyu dai na zargin junansu da kaiwa yankunan fararen hula farmaki da gangan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.