EU ta mara baya ga 'yan takarar Najeriya da Korea a shugabancin WTO
Wallafawa ranar:
Kasashen Turai sun bayyana goyan bayan su ga 'yan takara biyu mata da ke neman shugabancin Hukumar Kasuwanci ta Duniya domin ganin daya daga cikin su ta samu jagorancin hukumar.
Jakadun kasashen Turai sun bayyana fatar su na ganin Ngozi Okonjo-Iweala, tsohuwar ministar Najeriya ko Yoo Myung-hee, shugabar kasuwancin Koriya ta kudu ta samu kujerar bayan wani taro da suka yi a Brussels.
Yau ake saran hukumar ta rage yawan Yan takarar da ke neman kujerar zuwa mutum biyu daga cikin 8 da ke fafutukar ganin sun maye gurbin Roberto Azevedo wanda ya sauka daga kujerar a watan jiya.
Zabin Okonjo-Iweala zai bai wa Afirka damar rike kujerar a karon farko, ganin yadda nahiyar Turai ta rike kujerar sau 3, yayin da Oceania da Asia da Kudancin Amurka suka rike kujerar sau guda-guda.
Ana saran bayyana wanda ya samu nasara ne a watan Nuwamba.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu