Nobel

Mutanen da suka gano 'Black Hole' sun lashe Nobel

Wasu masana kimiya uku sun lashe kyautar Nobel saboda binciken da suka gudanar wajen gano Bakin Rami na Black Hole a sararin samaniya.

Roger Penrose da Reinhard Genzel da Andrea Ghez da suka lashe Kyautar Nobel.
Roger Penrose da Reinhard Genzel da Andrea Ghez da suka lashe Kyautar Nobel. Nobel Prize
Talla

Masana kiminiyan da suka hada da Roger Penrose na Birtaniya da Reinhard Genzel na Jamus da kuma Andrea Ghez ta Amurka sun lashe kyautar ce saboda jajircewarsu wajen gano daya daga cikin manyan abubuwan al’ajabi a duniya kamar yadda Kwamitin Kyautar Nobel ya bayyana.

Penrose mai shekaru 89, ya samu karramawar ce kan kokarin da ya yi na nuna wa duniya cewa, alakar maganadisu da sauran halittu ne ta kai ga gano bakin ramin na Black Hole, yayin da Genzel da Ghez aka karrama su bayan sun gano cewa, kwayoyin halittun zarra da ido ba ya iya gani da kuma wasu karikitai masu nauyi sune suka mamaye duniyar taurari.

Ghez ita ce mace ta hudu a tarihin duniya da ta samu kyautar karramawa ta Noble tun lokacin da aka fara bada ita a shekarar 1901.

Gwarzuwar ta shaida wa Kamfanin Dillancin Labaran Faransa AFP cewa, tana matukar murna da samun wannan karramawa, abin da ta ce, zai yi tasiri ga rayuwar ‘yan mata masu tasowa da ke sha’awar shiga fagen kimiya.

Shi dai wannan Black Hole din wani sashi ne a sararin samaniya, inda kwayoyin halitun zarra suka cure wuri guda don samar da wani fage mai nauyi da ke hana ratsawar haske.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI