Azerbaijan-Armenia

Turkiya ta ki amsa kiran NATO don sasanta rikicin Azerbaijan da Armenia

Shugaban Turkiya Recep Tayyib Erdogan ya ki amsa bukatar kungiyar tsaro ta NATO da ta nemi ya yi amfani da karfin fada ajin da ya ke da shi wajen shiga tsakani don sasanta rikicin Azerbaijan da Armenia wanda kawo yanzu ya lakume rayukan kusan mutum 300.

Shugaba Recep Tayyip Erdogan ya ce wajibi ne yankin Karabakh ya koma mazauninsa karkashin Azerbaijan kafin sasanta rikicin bangarorin biyu.
Shugaba Recep Tayyip Erdogan ya ce wajibi ne yankin Karabakh ya koma mazauninsa karkashin Azerbaijan kafin sasanta rikicin bangarorin biyu. Presidential Press Office/Handout via REUTERS
Talla

Tun a jiya Litinin ne babban sakataren kungiyar ta NATO Jens Stoltengerg yayin ganawarsa da ministan harkokin wajen Turkiya Mevlut Cavusoglu ya nemi kasar ta yi amfani da karfin ikonta wajen sasanta rikicin kasashen biyu.

Sai dai sa’o’I kalilan bayan kiran na NATO, kafofin labarai sun ruwaito shugaba Recep Tayyib Erdogan na kira ga Azerbaijan da ta kara kaimi don ganin ta kwace yankin na Nagorny Karabakh da ya balle daga hannunta yayin yakin 1990 tsakaninta da Armenia da ya kai ga mutuwar mutum dubu 30.

Cikin kalaman Erdogan matukar ba a mayar da yankin na Karabakh inda ya ke tun asali ba sam babu batun sasantawa a rikicin ko da ya ke yanzu haka ministan harkokin wajen Kasar ya isa Azerbaijan don tattaunawa da shugaba Ilham Aliyev.

Shugaba Erdogan wanda ya ke fuskantar takun saka da takwarorinsa mambobin NATO bayan matakinsa na sayen wasu makamai daga Rasha, ya ce a ko da yaushe su na goyon bayan Azerbaijan har zuwa abin da hali zai yi game da rikicin, inda shugaba Ilham Aliyev ke cewa wajibi ne Armenia ta janye dakarun da ta girke a wajen yankin na Karabakh gab da Azeris.

Kasashen biyu dai sun zargi junansu kan farmakar fararen hula, dai dai lokacin da aka shiga kwana na 9 da fara rikicin wanda ke kokarin komawa yaki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI