Amurka

Amurkawa sun fi son Biden ya zama shugaban kasa

Wata sabuwar kuri’ar jin ra’ayin jama’a ta nuna cewa, dan takarar shugabancin Amurka na jam’iyyar Democrat Joe Biden, ya bai wa shugaba Donald Trump rata mai yawa a daidai lokacin da ya rage kasa da wata guda a gudanar da zaben kasar.

Joe Biden da Donald Trump.
Joe Biden da Donald Trump. Studio Graphique FMM
Talla

Sabuwar kuri’ar wadda gidan talabijin na CNN ya gudanar a fadin Amurka, ta nuna cewa, kashi 57 na Amurkawar da suka cancaci yin zabe, sun ce, suna goyon bayan Biden, yayin da kashi 41 suka nuna goyon bayansu ga Trump.

An gudanar da kuri’ar jin ra’ayin jama'ar ne bayan muhawarar da ‘yan takarar biyu suka tafka da kuma jinyar cutar Covid-19 da shugaba Trump ya yi.

Kuri’ar ta nuna cewa, Biden ya samu rinjaye a muhimman wurare duk da cewa, wannan kuri’ar ba ta hasashen yadda ainihin zaben zai kaya, amma dai tana bayyana inda ra’ayoyin masu zabe suka karkata.

Ana ganin masu kada kuri’ar sun fi son Biden ne fiye da Trump saboda wasu batutuwa da suka hada da cutar coronavirus da kiwon lafiya da nuna wariyar launi da nadin allkalan kotun koli da dai makamantansu.

Kazalika masu kada kuri’ar na ganin cewa, Biden shi ne ya fi dacewa wajen hada kan Amurkawa tare da kuma kare kasar daga fuskantar barazanar cutarwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI