Karin mutane miliyan 115 za su fada kangin talauci - Bankin Duniya

David Malpass, shugaban Babban Banakin Duniya
David Malpass, shugaban Babban Banakin Duniya Reuters

Bankin Duniya ya yi gargadin cewar annobar korona dake cigaba da yiwa duniya illa yanzu haka, zata jefa akalla mutane miliyan 115 cikin tsananin talauci a wannan shekara ta 2020.

Talla

Wannan adadi da Bankin duniya ya gabatar ya zarce hasashen da yayi a watan Agusta, inda ya bayyana cewar mutane miliyan 100 ake zaton zasu fuskanci tsananin talauci sakamakon wannan annoba, yayin da sabon rahotan yace nan da shekara mai zuwa adadin na iya tashi zuwa miliyan 150 wadanda zasu dinga rayuwa kasa da Dala biyu kowacce rana.

Shugaban Bankin David Malpass ya sanar da cewar radadin wannan annobar da koma bayan tattalin arzikin duniya zai sanya kasha daya bisa 4 na al’ummar duniya cikin mawuyacin hali.

Bankin yace wadannan alkaluma da ya gabatar ya biyo bayan sakamakon binciken da kwararrun sa suka gudanar, wanda ke danganta talaucin da rashin ayyukan yi da rufe masana’antu da katsewar harkokin kasuwanci saboda illar cutar korona.

Bankin yace wannan matsalar zata hana samun nasarar cimma muradun karni na kawar da talauci a duniya nan da shekarar 2030 kamar yadda Majalisar Dinkin Duniya ta tsara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI