China

Kasashen duniya sun shigar da karar China saboda Musulmi

Kasashen duniya 39 sun sanya hannu kan wata wasikar da suka gabatar wa Majalisar Dinkin Duniya, inda suke bukatar China da ta daina azabtar da Musulmi 'yan kabilar Uighur da ke yankin Xijiang.

Wasu da ke zanga-zangar adawa da cin zarafin Musulmin Uighur na China.
Wasu da ke zanga-zangar adawa da cin zarafin Musulmin Uighur na China. David Cliff/SOPA Images/LightRocket via Getty Images
Talla

Jakadan Jamus a Majalisar Christoph Heusgen ya ce, suna bukatar China ta mutunta ‘yancin jama’a na yin addinin da suke bukata, sannan ta kare kananan kabilun da ke Xijiang da Tibet.

Cikin kasashen da suka sanya hannu kan wasikar har da Amurka da kasahsen Turai  da Albania da Bosnia da Canada da Haiti da Honduras da Japan da Australia da kuma New Zealand.

Masu bincike sun ce, sun bankado wurare sama da 380 da China ke amfani da su a matsayin gidajen yarin da take tsare 'yan kabilar Uighur a yankin Xijiang tare da azabtar da su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI