Ba'amurkiya Louise Gluck ta lashe kyautar Nobel bangaren adabi
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Kwamitin da ke bayar da kyautar girmamawa ta Nobel ya bayyana Ba'amurkiya Louise Gluck a matsayin wadda ta lashe kyautar bana ta bangaren adabi.
kwamitin da ke bayar da kyautar ta Nobel ya bayyana Gluck mai shekaru 77 a matsayin wadda ta yi fice wajen rera rubutun adabin da ta ke rubutawa, kuma zabin da aka mata ya bai wa mutane da dama mamaki.
Sakataren kwamitin Mats Malm ya ce ya yi magana da Gluck jim kadan kafin bayyana wanda ya lashe kyautar, inda ta bayyana mamaki wajen zabin da aka mata, kafin bayyana farin cikin ta.
Gluck ce mace ta 4 da ta taba lashe kyautar a wannan bangaren a cikin shekaru 10, bayan Olga Tokarczuk da Svetlana Alexievich da kuma Alice Munro.
Daga cikin ayyukan da ta yi akwai ‘The Triumph of Achilles’ a shekarar 1985 da ‘Arafat’ a shekarar 1990 da ‘Averno’ a shekarar 2006.
Ya zuwa yanzu mata 16 kawai suka taba lashe kyautar Nobel daga cikin mutane 117 tun lokacin da aka fara bada lambar girmamawar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu