UNICEF-WHO

Kowacce dakika 16 ana samun mace guda da ke barin ciki a Duniya- rahoto

Rahoton ya bayyana fargaba kan yiwuwar annobar Covid-19 ta kara yawan matan da ke barin ciki a kowacce rana.
Rahoton ya bayyana fargaba kan yiwuwar annobar Covid-19 ta kara yawan matan da ke barin ciki a kowacce rana. Reuters

Wani rahotan hadin gwuiwa tsakanin Majalisar Dinkin Duniya da WHO da kuma  Bankin Duniya baya ga UNICEF ya ce cikin kowacce dakika 16 ana samun mace guda da kan yi barin ciki, abin da ke sanadiyyar mutuwar 'yan tayin jarirai miliyan 2 kowacce shekara.

Talla

Alkaluman rahoton ya nuna cewa kashi 84 na mace-macen 'yan tayin ana samun su ne a kasashe marasa karfi da masu tasowa, inda duk jarirai 3 cikin hudu da ke mutuwa ake samunsu a ko dai yankin kudu da saharar Afrika ko kuma kudancin Asia.

Henrietta Fore ta kungiyar UNICEF ta bayyana arasar 'yan tayin jariran lokacin da ake goyan ciki a matsayin babban tashin hankali ga iyalai, wanda ta ce sai wanda abin ya shafa ne kadai zai iya bayani akai.

Jami’ar ta ce a cikin kowacce dakika 16 wata mace a wani wuri na fuskantar wannan matsala da bata iya misaltuwa, wanda ke sanya mata da iyalai da kuma al’umma cikin tashin hankali.

Fore ta ce ana iya kaucewa mutuwar irin wadannan 'yan tayi ko kuma kawar da barin da mata masu juna biyu ke yi ta hanyar bai wa mata masu juna biyu kulawar da ta dace, kulawar da za a iya samu kadai daga mutanen da suka samu horo na musamman kan hakan.

Rahoton hukumomin 4 ya kuma bayyana fargabar yiwuwar annobar Covid-19 ta kara yawan barin cikin da Matan ke samu a sassan duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.