Bakonmu a Yau

Tattaunawa da Alhaji Garba Sulaiman Krako Saminaka kan bayar da belin dan sandan da ya kashe George Floyd a Amurka

Wallafawa ranar:

Rahotanni daga kasar Amurka na cewa dan sandan nan farar fata Derek Chauvin, da ake zargi da kisan wani bakar fata George Floyd, al’amarin da ya haifar da kazamin bore a sassan kasar, yanzu haka dai an bada belin sa kuma har ya fice daga gidan yari da ake tsare da shi.An bada belin dan sandan ne akan kudi Dalan Amurka miliyan guda, kan hakan Garba Aliyu Zaria ya tuntubi Alhaji Garba Sulaiman Krako Saminaka mazaunin Amurka da ke bibiyar lamarin kuma ga bayanin da ya yi mana.

Kisan bakar fatar a Minneapolice ya haddasa zazzafar zanga-zanga a ilahirin sassan kasar.
Kisan bakar fatar a Minneapolice ya haddasa zazzafar zanga-zanga a ilahirin sassan kasar. REUTERS/Nicholas Pfosi