Faransa-Mali

Cisse da Petronin sun kubuta daga 'yan bindigar Mali

Sophie Pétronin a fadar gwamnatin Mali bayan sakinta.
Sophie Pétronin a fadar gwamnatin Mali bayan sakinta. Présidence malienne / AP

Rahotanni daga Mali sun ce an saki wata Bafaranshiya ma’aikaciyar agaji, Sophie Petronin mai shekaru 75 da aka yi garkuwa da ita tun shekarar 2016 tare da shugaban 'yan adawan kasar Soumaila Cisse mai shekaru 70, yayin da shugaban Faransa Emmanuel Macron ya zanta da matar ta wayar tarho, kafin ya gana da ita wani lokaci a yau Juma'a. 

Talla

Ofishin shugaban sasar Mali ya fara sanar da sakin Petronin da Cisse da ake zargin kungiyar Al Qaeda da sace su kafin daga bisani suka sauka filin jirgin saman Bamako.

Wannan na zuwa ne bayan sakin mutane akalla 100 daga cikin wadanda ake zargi ko kuma aka yankewa hukuncin aikata laifuffukan masu nasaba da ta’addanci.

Ita dai gwamnatin ba ta yi bayani kan yadda aka saki wadannan mutane biyu ba, kuma ya zuwa yanzu babu cikakken bayani game da halin lafiyarsu.

Ita dai Petronin an sace ta ne ranar 24 ga watan Disamban shekarar 2016 a Gao da ke arewacin kasar, kuma ita ce 'yar Faransa ta karshe da ake garkuwa da ita a duniya.

Shi kuwa Cisse, wanda sau uku yana takarar shugaban kasa, an sace shi ne ranar 25 ga watan Maris lokacin da yake yakin neman zabe a Niafounke.

Rahotanni sun ce an kuma saki wani limamin Kirista Pier Luigi Maccali da aka sace a Nijar a shekarar 2018 tare da Nicola Chiacchio da ta bata a bara lokacin da take tafiya akan keke.

Kasar Mali ta fada cikin rikicin kabilanci da addini tun daga shekarar 2012, rikicin da ya lakume rayukan dubban mutane.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.