Hukumar Abinci ta Duniya ta lashe kyautar Nobel

Hukumar Abinci ta Majalisar Dinkin Duniya
Hukumar Abinci ta Majalisar Dinkin Duniya UPDEGRAFF / US NAVY / AFP

Hukumar samar da Abinci ta Majalisar Dinkin Duniya WFP ta bi sahun fitattun wasu mutane wajen lashe lambar yabo ta Nobel, sakamakon gudunmawar ta wajen yakar matsalar Yunwa a sassan duniya.

Talla

Yayin bayyana nasarar hukumar ta WFP a birnin Oslo na kasar Norway, shugaban kwamitin bada lambar yabon ta Nobel Berit Riess-Andersen, ya ce annobar coronavirus ta kara munin bala’in yunwar da dama tuni miliyoyin mutane ke fuskanta a kasashe daban daban, inda yace kalubalanci hukumomi da suka kara zama wajen daukar matakan fidda mutane daga kangin.

Riess-Andersen ya kara da cewa, suna fatan ganin mutanen duniya sun karkata idanunsu don ganin halin yunwa da wasu ke ciki a kasashin duniya.

Hukumar samar da Abinci ta Majalisar Dinkin Duniya itace kan gaba wajen ayukan jinkai a duniya, inda take taka muhimmiya rawa wajen samar da abinci ga mutane sama da miliyan 690, dake fama da yunwa, masamman Koriya ta Kudu da Yaman, da wasu kasashen Afirka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI