'Yan gudun hijira kussan miliyan 3 ke warwatse a kasashen duniya - MDD

Sansanin 'yan gudun hijira a Girka
Sansanin 'yan gudun hijira a Girka REUTERS/Alkis Konstantinidis

Majalisar Dinkin Duniya ta ce ‘yan gudun hijira kusan miliyan 3 ne yanzu haka suka kasa komawa kasashensu, inda suke cigaba da zama makale a sansanoni daban daban da ke sassan duniya, saboda matakan da gwamnatocin kasashe suka dauke na takaita zirga-zirga saboda annobar coronavirus.

Talla

Cikin sabon rahoton, Hukumar kula da ‘Yan gudun Hijira ta Majalisar Dinkin Duniyar IOM, ta gargadi kasashe da su gaggauta hada gwiwa wajen warware matsalar, don kaucewa jefa miliyoyin mutanen cikin tagayyara.

Rahoton ya ce yankunan gabas ta Tsakiya da arewacin Afrika ke da kason ‘yan ci ranin mafi yawa da adadin miliyan 1 da dubu 260, sai kuma Asiya da Pacific masu ‘yan gudun hijirar dubu 977.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.