Trump-Coronavirus

Trump zai jagoranci taron siyasa karon farko bayan kamuwa da Covid-19

A karon farko bayan fara jinyar cutar Covid-19 fiye da mako guda da ya gabata, shugaban Amurka Donald Trump zai jagoranci taron jama’a a fadar White House a wani yunkuri na nunawa duniya yadda ya murmure daga cutar dai dai lokacin da ake ci gaba da jita-jita kan halin lafiyar tasa.

Shugaban Amurka Donald Trump yayin jawabinsa daga farfajiyar saman fadar White House.
Shugaban Amurka Donald Trump yayin jawabinsa daga farfajiyar saman fadar White House. Win McNamee/Getty Images/AFP
Talla

Taron na yau Asabar dai na da nufin nunawa duniya kwarin jikin da Donald Trump ke da shi don ci gaba da gwagwarmayar yakin neman zaben shugabancin kasar, inda kai tsaye zai yi jawabin ga dubunnan mahalarta taron wanda aka yi masa suna da gangamin lumana bisa tanadin doka.

A ranar 2 ga watan Oktoba ne gwaji ya tabbatar Trump ya kamu da coronavirus dalilin da ya sanya shi kwanciya a asibiti tsawon kwanaki 3 gabanin ya sallami kansa daga asibitin ba tare da sahalewar likitoci ba, batun da ya haddasa cece-kuce.

Zuwa yanzu dai gwaji bai tabbatar da Donald Trump ya rabu da cutar ba sai dai bayanai sun ce ya daina nuna alamominta dai dai lokacin da cutar ta hallaka Amurkawa fiye da dubu 210.

Ko a jiya Juma’a kakakin fadar ta White House ta ce za a sake yiwa shugaban gwajin covid-19 kuma matukar sakamako ya nuna yana dauke da cutar hakan na nufin bashi da zarafin shiga dandazon jama’a.

Haka zalika kawo yanzu fadar ta White House ba ta bayar da izinin gudanar da taron na Trump ba, sai dai tuni kwamitin yakin neman zabensa ya kammala shela da kuma gayyatar mahalarta taron don ganewa idonsu shugaban tare da jin jawabinsa.

Kwamitin yakin neman zaben na Trump ya sanar da shirin gudanar da wani gagarumin gangami a tsakiyar Florida Litinin mai zuwa gabanin makamancinsa ranar Talata a Pennsylvania kana wani na daban a Iowa ranar Laraba.

Cikin kalaman Donald Trump ya bayyana cewa sakamakon gwajinsa na biyu kan cutar bai fito ba, amma tuni ya dai na shan magunguna la’akari da yadda ya ke jin kwarin jikinsa kuma tuni ya daina ganin alamomin cutar ta Covid-19.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI