Korea ta Arewa

Gwajin makamin Korea ta Arewa abin takaici ne- Amurka

Gwajin makamin Korea ta Arewa.
Gwajin makamin Korea ta Arewa. KCNA via REUTERS

Wani babban jami’in Amurka ya bayyana gwajin makamin da korea ta Arewa ta yi jiya Asabar a matsayin babban abin takaici da ya sabawa yarjejeniyar da ke tsakaninsu wadda ta amince da kwance ilahirin makaman da ita Korean ta mallaka baya daina gwajin makamanta makaman masu hadari.

Talla

Babban Jami'in na Amurka wanda kamfanin dillancin labaran Faransa bai kama sunanshi ba, ya ce sam Korea ta Arewa ta keta dokokin yarjejeniyar da ke tsakaninta da Washington duk da ya ke tun a wancan lokaci kasashen biyu ba su fito sun bayyana abin da yarjejeniyar ta kunsa ba.

A jiya Asabar ne Korea ta Arewan bisa jagorancin Kim Jong Un ta gudanar da wani gagarumin atisayen Soji inda cikinsa ta aiwatar da gwajin makamin nukiliya kirar ICBM mai cin dogon zango.

Masana sun bayyana kirar makamin samfurin ICBM a jerin mana nukiliya mafiya hadari da ke iya tafiyar kilomita dubu 24 cikin sa’a guda.

Tun kafin yanzu dai Kim Jong Un ya gabatar da gwaje-gwaje makamai daban-daban amma Donald Trump ya ce sam basu saba ka'ida ba.

Tattaunawa tsakanin kasashen biyu ta tsaya ne tun bayan ganawar Trump da Kim bara a Hanoi wadda Amurka ta nemi janyewa Korean takunkuman da ke kanta amma bisa sharudda, ganawar da kawo yanzu ba a sake makamanciyarta ba.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.