Amurka

Ina dauke da garkuwar corona a jikina-Trump

Shugaban Amurka Donald Trump
Shugaban Amurka Donald Trump Leah Millis/Reuters

Shugaban Amurka Donald Trump ya ayyana kansa a matsayin mai dauke da garkuwar Covid-19, wanda kuma ya shirya komawa fagen-daga a daidai lokacin da abokin hamayyarsa Joe Biden ya yi masa zarra a fafutukar neman kujerar fadar White House.

Talla

A ranar Asanar da ta gabata ne, likitan Trump ya wanke shi domin komawa fegen-daga, yana mai cewa ce, shugaban ba ya tattare da hatsarin yada cutar coronavirus duk da cewa, har yanzu ba a ayyana shi ba a matsayin wanda ya rabu da ita ba.

Shugaba Trump ya shaida wa gidan talabijin na Fox News cewa, yana dauke da garkuwar cutar, amma babu tabbaci ko kuma shaida kan wannan ikirari nasa.

Kalmar garkuwa da shugaban ya yi amfani da ita na nufin cewa, yana dauke da wata kariya a jikinsa mai hana shi kamuwa da cutar.

Wasu masana kimiya sun ce, mutanen da suka warke daga Covid-19 ka iya samun garkuwarta a jikinsu na tsawon watanni ko kuma dogon lokaci. Kodayake ana kan ci gaba da gudanar da bincike kan batu.

A yayin hirar tasa da Foxe News, Trump ya shaida wa Amurkawa cewa, ‘lallai yanzu suna da shugaban da ba ya nokewa kamar abokin hamayyarsa,’ kalaman da ke zama shagube ga Joe Biden na Jam’iyyar Democrat wanda ke taka-tsan-tsan a yakin neman zabensa saboda annobar corona.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI