Armenia-Azerbaijan

Zaman lafiyar Armenia da Azerbaijan ya gamu da cikas

Kasashen Azerbaijan da Armenia na zargin juna da kai wa fararen hula farmaki
Kasashen Azerbaijan da Armenia na zargin juna da kai wa fararen hula farmaki Bulent Kilic / AFP

Fatan ganin dorewar shirin tsagaita wuta tsakanin Armenia da Azerbaijan wadda Rasha ta jagoranta ya samu koma baya sakamakon zarge-zargen da kasashen biyu ke yi wa juna na kai hari kan fararen hula.

Talla

Ma’aikatar Harkokin Wajen Azerbaijan ta sanar cewa, hare-haren sama da dakarun Armenia suka kai cikin dare a birnin Ganja sun yi sanadiyar kashe mutane 7 da kuma raunata wasu 33 cikinsu har da kananan yara, kasa da sa’oi 24 bayan kulla yarjejeniyar tsagaita wutar.

Masu aikin agaji sanye da jajayen huluna sun yi ta hakar burabuzai domin ceto wadanda gine-gine suka danne.

Sai dai Ma’aikatar Tsaron Armenia ta yi watsi da zargin, inda ta ce dakarunta na mutunta yarjejeniyar, kuma sojin Azerbaijan ne suka kai mata harin sama.

Kakakin shugaban Karabakh Vahram Poghosyan ya ce harin da aka kai garin Stephanakert ya saba wa yarjejeniyar da suka kulla wadda ta kunshi tsagaita wuta da musayar fursinoni.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.