Amurka

Democrat ta soki shirin nadin shugabar Alkalan kotun Koli gabanin zabe

Mai shari'a Amey Coney Barrett a gaban Majalisar Dattijan Amurka yayin tafka muhawara kan tantanceta a matsayin magajiyar Ruth Bader Ginsburg da ta rasu ranar 26 ga watan jiya
Mai shari'a Amey Coney Barrett a gaban Majalisar Dattijan Amurka yayin tafka muhawara kan tantanceta a matsayin magajiyar Ruth Bader Ginsburg da ta rasu ranar 26 ga watan jiya Win McNamee/Pool via REUTERS

Majalisar Dattijan Amurka ta fara zaman tantance mai shari’a Amy Coney Barrett domin cike gurbin Ruth Bader Ginsburg da ta rasu ranar 26 ga watan jiya.Yayin fara zaman an samu rarrabuwar kawuna tsakanin 'ya'yan Jam’iyyar Republican ta shugaba Donald Trump da 'yan democrat da ke bukatar jinkirta tantancewar har zuwa bayan zaben watan gobe.

Talla

Shugaban kwamitin shari’a na Majalisar Dattawan Amurka Sanata Lindsey Graham ya ce babu wani laifi dangane da matakin nada mai shari’ar a dai dai lokacin da ake shirin gudanar da zabe.

Sanata Graham ya kafa hujja da cewa ita kanta Ginsburgh yayinda ta ke amsa wasu tambayoyi shekarun baya kan makamancin nadin ta ce shugaban kasa nada cikakkiyar damar yin nadin a kowanne lokaci domin kuwa, wa’adin shekaru 4 ya ke dasu akan mulki ba 3 ba, don haka babu abinda ya sabawa dokokin kasa dangane da makamancin nadin.

Acewar Sanata Graham wannan gibi ne da aka samu sakamakon rashin fitacciyar mace kuma a yanzun za a cike gurbin da aka samu da da wata fitacciyar macen, yana mai cewa majalisar dattijan na gudanar da aikin ta ne bisa dokokin kasa.

Sai dai Sanata Dianne Feinstein daga Jam’iyyar Democrat ta ce tarihi ne ke maimaita kan sa, domin lokacin Obama an samu gibi kusa da zabe, amma 'yan Republican suka bukaci jinkirta nadin, saboda haka yanzu ya zama wajibi suma su mutunta wancan alkawari.

Sanata Feinstein karkashin wancan alkawari da aka kulla lokacin mulkin Barrack Obama na Democrat an aminta da cewa idan har an samu gibi a shekarar karshe na wa’adin Trump, dole ne a jira har sai an kammala zabe mai zuwa.

Sanatar ta ce ya dace 'yan Republican su mutunta wancan alkawari, domin bada damar jin ta bakin Amurkawa.

Acewarta bai dace Majalisar ta ci gaba akan nadin ba, har sai an kammala zabe, kuma shugaba mai zuwa ya shiga ofis.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI