Isra'ila
Isra'ila za ta bai wa Yahudawan Habasha dubu 2 matsugunai
Gwamnatin Israila ta amince da shirin bai wa Yahudawa 2,000 da ke zama Habasha damar komawa kasar, matakin da ya gamu da suka.
Wallafawa ranar:
Talla
Su dai wadannan Yahudawa na daga cikin iyalan Falash Mura, jikokin Yahudawan Habasha da suka koma addinin Kirista a karni na 18 da 19.
Yahudawan Israila na kallon wadannan Yahudawan Habasha a matsayin wadanda suka saba da su, kuma wasu daga cikin su na adawa da basu damar komawa kasar.
Firaminista Benjamin Netanyahu ya shaidawa Majalisar ministocin sa cewar lokaci yayi da za’a baiwa wadannan mutane damar komawa gida.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu