WHO-Corona

WHO ta gargadi Duniya kan bai wa cutar Covid-19 damar yaduwa

Shugaban hukumar lafiya ta duniya WHO, Tedros Adhanom Ghebreyesus.
Shugaban hukumar lafiya ta duniya WHO, Tedros Adhanom Ghebreyesus. Christopher Black/WHO

Shugaban Hukumar Lafiya ta Duniya Tedros Adhanom Gebreyesus ya yi gargadi kan barin cutar korona ta yadu da zummar samun sinadarin garkuwa daga illar ta, inda ya ke cewa hakan ya saba ka’ida.

Talla

Tedros ya gargadi wasu kasashen da ke barin cutar ta yadu yadda ta ke so har zuwa lokacin da mutane za su samu garkuwar jikin da zai hana cutar yi musu illa.

Shugaban hukumar ta WHO ya ce babu wani lokaci a tarihin duniya da aka bar mutane su samarwa kan su garkuwa don kariya daga annoba irin wannan.

Ya zuwa yanzu korona ta kama mutane sama da miliyan 37 da rabi a duniya, kuma ta kashe sama da miliyan guda.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI