Amurka

Amurka ta yi kashedi kan karbar tallafin China da Rasha

Sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo ya bukaci cibiyoyin bincike na kasar da su kauce wa rufa-rufa game da tallafin kudaden da suke samu daga kasashen waje, inda ya gargade su game da karbar tallafi daga China da Rasha.

Sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo.
Sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo. Mike Segar/Reuters
Talla

Pompeo ya yi kira ga wadannan cibiyoyin binciken da ke neman dasawa da ma’aikatarsa da su bayyana hanyoyin da suke samun kudaden tallafinsu domin sanin kasashen da ke hulda da su.

A ‘yan watannin baya gwamnatin shugaba Donald Trump ta zafafa matsin lamba a kan China, inda Pompeo ya kara sanya ido a kan cibiyoyin da yake ganin China na amfani da su wajen yi wa Amurka katsalandan a harkokinta.

A watan Agusta Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta tsaurara ka’idoji kan cibiyoyin koyar da harsunan kasar Sin da China ta kafa a jami’o’in Amurka, wadanda masu caccaka suka ce suna wanzuwa ne don yada manufofin kwamisanci.

Cibiyoyin binciken Washington sun kasance tamkar mafaka ne ga kwararrun da suka yi murabus daga aikin gwamnati, kuma suke neman tallafin gudanar da ayyukansu tsawon gwamman shekaru, sai dai yawancin tallafin da suke samu na zuwa ne daga kasashen da ke jituwa da Amurka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI