Saudiya

An hana Saudiya shiga sahun masu kare jama'a

Yarima Mai Jiran Gadon Saudiya Mohammed bin Salman
Yarima Mai Jiran Gadon Saudiya Mohammed bin Salman Mandel Ngan/Pool via REUTERS/File Photo

Saudiya ta gaza samun kujera a Hukumar Kare Hakkin Bil’adama ta Majalisar Dinkin Duniya, yayin da aka zabi China da Rasha domin yin wa’adin shekaru uku a hukumar.

Talla

Kungiyoyin Kare Hakkin Bil’adama sun yi murna da yadda aka hana Saudiya zama mamba a hukumar, lamarin da ya kawo mata cikas a yunkurinta na farfado da martabarta a idon kasashen duniya.

Kungiyar Human Rights Watch ta ce, rashin zaben Saudiya na a matsayin kyamata ga kasar wadda ta yi kaurin suna karkashin shugabancin Yarima Mai Jiran Gado Mohammed bin Salman.

An dai gudanar da zaben ne domin cike kujeru 4 a hukumar wadda ke shan caccaka daga kungiyoyin kare hakkin bil’adama da Amurka saboda zargin ta da zaben kasashen da ke cin zarafin jama’a.

Kisan gillar da jami'an Saudiya suka yi dan jaridan nan Jamal Kashogi a birnin Santanbul na Turkiya na cikin abin da ya kawo mata cikas a zaben.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.