Isra'ila-Falasdinu

Isra'ila za ta gina gidaje fin dubu 2 a yankin Falasdinu da ta ke mamaya

Kasar Israila ta amince da shirin gina sabbin gidajen Yahudawa dubu 2 da 166 a Gabar Yamma da Kogin Jordan, irin sa na farko tun bayan kulla yarjejeniyar hulda da wasu kasashen larabawa.

Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu.
Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu. Sebastian Scheiner/Pool via REUTERS
Talla

Daukar wannan matakin na zuwa ne kasa da wata guda da yadda Isra'ilar ta kulla hulda da Daular Larabawa da Bahrain a wani biki da ya gudana a Amurka wanda ya ce Israilar za ta dakatar da shirin mamaye wani yanki na Gabar Yamma da Kogin Jordan.

Kungiyar agaji ta ‘Peace Now’ ta ce bayyana wannan shirin na Firaminista Benjamin Netanyahu ya dada fito da adawar sa na kafa kasar Falasdinu da kuma dakushe shirin sa na kulla karin yarjeniyoyi da wasu kasashen larabawan.

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Jordan, Daifalla Ali Alfayez ya bayyana matakin na Israila a matsayin abin takaici kuma haramtacce, yayin da mai magana da yawun shugaban Falasdinawa Nabil Abu Rudeina ya ce Israilan ta dauki matakin ne saboda rungumar ta da wasu kasashen laraba suka yi.

Majalisar Dinkin Duniya da wasu manyan kasashen duniya irin su Faransa da Birtaniya da Jamus na kallon gini a yankunan Falasdinawan a matsayin haramtacce.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI