Chadi-Boko Haram

Jamus ta bada tallafin rage radadin yakin Boko Haram

Wasu daga cikin mutanen da rikicin Boko Haram ya raba da muhallansu
Wasu daga cikin mutanen da rikicin Boko Haram ya raba da muhallansu SIA KAMBOU / AFP

Kasar Jamus ta bada karin tallafin Euro miliyan 15 domin inganta rayuwar mutanen da ke zaune a zagayen Tafkin Chadi da rikicin Boko Haram ya daidaita.

Talla

Wannan tallafin na daga cikin alkawuran da kasar ta yi na bada gudumawar samar da tsaro a yankin da kuma samar da kayan more rayuwa da inganta rayuwar al’ummomin da ke yankin.

Jakadiyar Jamus a Najeriya, Birgitt Ory ta ce wannan gudumawa na daga cikin taimaka wa abokan tafiyarsu na Najeriya kuma ana saran kasashen kewayn  Tafkin Chadi da suka hada da Nijar da Kamaru da Chadi za su ci gajiyar gudunmawar.

Ory ta ce tallafin na daga cikin wadanda kasar Jamus da kungiyar kasashen Turai da Netherlands da Sweden da kuma Birtaniya suka yi alkawari domin sake tsugunar da mutanen da ke yankin Tafkin Chadi gaba daya.

Shirin na kuma samun taimakon Majalisar Dinkin Duniya da kungiyar kasashen Afirka ta AU.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI