Coronavirus

Turai na daukar matakan takaita walwalar jama'arsu bayan tsanantar Covid-19

Kasashen Nahiyar Turai na ci gaba da daukar matakan takaita walwalar jama’arsu don dakile cutar coronavirus da ke ci gaba da yaduwa a karo na biyu, dai dai lokacin da shirin yaki da cutar ya gamu da babban gibi bayanda guda cikin manyan kamfanonin da ke aikin samar da maganin cutar ya sanar da dakatar da gwajin maganin cutar da ya ke gudanarwa.

Zuwa yanzu mutane fiye da miliyan 37 suka kamu da Coronavirus a sassan Duniya.
Zuwa yanzu mutane fiye da miliyan 37 suka kamu da Coronavirus a sassan Duniya. Paul Faith / AFP
Talla

Cutar wadda ke ci gaba da yaduwa tamkar wutar daji a sassan duniya, galibin kasashen Turai na fuskantar zagaye na biyu na cutar inda yanzu haka kasashen Faransa Birtaniya da kuma Netherland baya ga Jamus suka dauki matakan takaita walwalar jama’arsu a wani yunkuri na dakile cutar, gabanin kammala samar da maganinta zuwa karshen shekarar nan kamar yadda hukumomin lafiya suka alkawarta.

A bangare guda itama China tuni ta fara aikin gwajin wani yanki mai al’umma miliyan 9 bayan samun daidaikun da suka koma kasar daga ketare dauke cutar, dai dai lokacin da jumullar mutanen da cutar ta kama a sassan duniya ke miliyan 37 ciki har da fiye da miliyan 1 da dubu 100 wadanda cutar ta kashe.

Matakin katafaren kamfanin magunguna na Johnson and Johnson a jiya Talata wajen dakatar da gwajin nau’in magungunan cutar 2 da ya ke shirin samarwa ya sanya rudani a kokarin da ake na samar da maganin cutar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI