Coronavirus

Karuwar masu Coronavirus a Turai abin damuwa ne- WHO

WHO ta ce duk da tsanantar cutar bai yi munin na watan Aprilu ba, amma halin da nahiyar ke ciki abin damuwa ne.
WHO ta ce duk da tsanantar cutar bai yi munin na watan Aprilu ba, amma halin da nahiyar ke ciki abin damuwa ne. © Czarek Sokolowski / AP Photo

Hukumar lafiya ta duniya ta ce karuwar adadin wadanda ke harbuwa da cutar coronavirus a nahiyar Turai abin damuwa ne matuka, sai dai lamarin bai yi muni kamar na watan Afrilu ba.

Talla

Shugaban Hukumar Lafiya ta Duniya a yankin Turai, Hans Kluge ya shaida wa wani taron manema labarai cewa wadanda ke harbuwa da wannan cuta ta Covid 19 karuwa suke a kullum, haka ma wadanda ke kwanciya a asibiti, sai dai ya ce yanayin bai kai wanda aka fuskanta a watannin Maris da Afrilu ba.

Ya kara da cewa ko da yake masu karuwa da cutar a wannan karon na ninkawa sau biyu ko uku a duk rana idan aka kwatanta da yadda yake a Afrilu, mace mace ya ragu har ninki biyar.

Ya ce dalilan da suka sanya aka samu karuwar adadin wadanda cutar ta Corona ta harba sun hada da matsa kaimi wajen gwaje gwaje a tsakanin matasa, haka kuma ana iya cewa mace mace sun ragu ne sakamakon yaduwa da cutar ta fi yi a tsakanin su matasan wadanda garkuwan jikinsu ke da inganci.

Sai dai Kluge ya kara da cewa, idan aka sassauta matakan kariya, adadin wadanda cutar za ta aika barzahun a watan Janairun 2021 zai ninka na watan Afrilun bana har sau biyar.

Ya karkare da cewa daukar matakai masu sauki kamar yawaita amfani da mayanin fuska da tsaurara dokar takaita taron jama’a zai ceto sama da rayuka dubu dari 2 da 80.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.