Saudiya ta bude filayen jiragen samanta ga wasu kasashen duniya 20

Kasar Saudiya ta maido da zirga-zirgan jiragen sama zuwa manyan kasashen duniya 20, bayan shafe watanni 7 dundum basa ganin kowa daga kasashen duniyar saboda fargaban bazuwar kwayar cutar korona.

Daya daga cikin filayen jiragen saman kasar Saudiya
Daya daga cikin filayen jiragen saman kasar Saudiya AFP/Getty
Talla

Manyan kasashen duniyar sun hada da su Amman, Dubai, Tunis, Cairo, Alexandria, Khartoum, Nairobi, Addis Ababa, Armsterdam, Frankfurt, Santambul, London, Madrid, Paris, Washington, Islamabad, Karachi, Kuala Lumpur da Manila.

Daga yau dinnan ne dai ake sa ran jiragen saman Saudiya su fara karakaina zuwa wadannan biranen kasashen duniya.

Tun a ranar 14 ga watan Maris, gwamnatin Saudiya ta dakatar da saukar jiragen sama cikinta daga kasashe, domin dakile yaduwar cutar coronavirus.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI